Mutanen dai an cafke su ne tare da hadin kan iyalan 'yan ta'addan da suka kai hare-haren a yankuna biyar na kasar dake arewa maso yamma, da suka hada da Kermanshah, Kurdistan, Azerbaïjan da kuma Tehran babban birnin kasar.
A yayin samamen da jami'an tsaron kasar suka kai an kuma gano bindigogi masu da kayayakin hada boma-bomai da kuma damara masu fashewa.
A wani labari kuma an cafke wani mutum wanda ba dan kasar Iran ba ne a lardin Mahchahr na Khouzestan wanda a cewar labarin shi ne ke taimakawa 'yan ta'addan da kayan aiki.
A jiya ne dai akayi jana'izar mutane 17 da suka rasa rayukansu a jerin hare-haren ta'ddancin da aka kai a ranar 7 ga watan nan a majalisar dokoki da kuma hubbaren Iman Khomeini wanda ya asassa Jamhuriya musulinci ta Iran.
A halinda ake ciki dai gwamnatin Iran da al'ummarta na ci gaba da samun sakwannin ta'aziyya daga kasashen duniya.288